A wannan rana, Mr. Arabi da ministan harkokin waje na kasar Masar Mohammad Amur sun gana da Mr. Abbas a birnin Ramallah da ke gabar yamma ta kogin Jordan. Daga baya kuma Mr. Arabi ya bayyana a yayin taron manema labaru, cewar har zuwa yanzu kasashen Larabawa daban daban ba su cika alkawarinsu na samar wa hukumar ikon al'ummar Palesdinu taimakon kudi Dalar Amurka miliyan 100 a ko wane wata ba.
Haka kuma Mr. Arabi ya ruwaito Abbas na cewa, Palesdinu na bukatar taimako ta fuskar tattalin arziki da goyon baya a siyasance, amma matsalar kudi da take fuskanta yanzu ta tilasta wa Palesdinu ta zabi taimakon kudi da farko. Don haka Arabi ya yi kira ga kasashen Larabawa da su cika alkawarinsu nan da nan, a kokarin taimakawa hukumar Palesdinu wajen tinkarar matsalar kudi mai tsanani da take fuskanta.(Kande Gao)