in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AL ta amince da kawancen bangarorin 'yan adawar kasar Siriya halastacciyar kungiyar da za ta wakilci jama'ar kasar Siriya
2012-11-13 16:50:07 cri
A ranar 12 ga wata, kungiyar hadin gwiwar kasashen Larabawa AL ta yanke shawara cewa, ta amince da kawancen bangarorin 'yan adawar kasar Siriya a matsayin halastacciyar kungiyar da za ta wakilci jama'ar kasar Siriya.

An yanke wannan shawara ce a gun taron ministocin harkokin waje na musamman na kungiyar AL da aka yi a ran 12 ga wata da dare a birnin Alkahira na kasar Masar, inda aka yi kira ga sauran bangarorin 'yan adawa na kasar Siriya da su shiga cikin wannan kawance, kuma an yi kira da a bayar da gudummawa a siyasance da ta kayayyaki ga kawancen.  

Bisa kundin tsarin mulkin M.D.D., kasashen Algeriya da Iraqi sun yanke shawarar rashin cikakken gamsuwa game da kudurorin mayar da kawancen bangarorin 'yan adawar kasar Siriya a matsayin halastacciyar kungiyar da za ta wakilci jama'ar kasar Siriya, kuma kasar Lebanon ta nuna ra'ayin ko in kula game da wannan kuduri.

Tuni a wannan rana, kungiyar hadin gwiwar kasashen Larabawa da ke yankin tekun Gulf GCC, ta ba da wata sanarwa, inda ta amince da kawancen bangarorin 'yan adawar kasar Siriya, da aka kafa kwanan baya a matsayin halastacciyar kungiyar da za ta wakilci jama'ar kasar Siriya.

A ranar 10 ga wata ne dai, karkashin taimako da goyon bayan kasashen Amurka, da Qatar, da Turkiyya da kungiyar kasashen Larabawa AL, bangarorin 'yan adawa na kasar Siriya suka sanar da kafa kawancen kungiyoyin a birnin Doha hedkwatar kasar Qatar, inda suka zabi shugabannin da za su ja ragamar hadaddiyar kungiyar. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China