in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da gangamin wayar da kai kan muhimmancin taron Brick a kasar Afrika ta Kudu
2013-02-24 16:18:13 cri
A ci gaba da shirye shiryen daukar bakuncin taron kungiyar kasashe 5 masu bunkasar tattalin arziki ta Brics, mahukunta a kasar Afirka ta Kudu sun shirya wani gangamin wayar da kan jama'a muhimmancin taron, da ma matsayin kasar cikin kungiyar.

Da yake jawabi yayin kaddamar da gangamin, ministan ma'aikatar kimiyyar da fasahar kasar Derek Hanekom, ya ce kasancewar kasar cikin wannan kungiya zai taimaka matuka wajen shawo kan kalubalolin da take fuskanta a fannin tattalin arziki. Haka nan ya kara da cewa ana fatan cimma nasarori masu yawa cikin tsahon lokaci, ciki hadda batun rage matsalar rashin ayyukan yi, da tafara, da kuma rashin daidaito tsakanin al'ummar kasar, baya ga burin da ake da shi na cimma buri kan muradin karni.

Daga nan sai ministan ya jaddada aniyar gwamnatin kasar mai ci, na inganta rayuwar al'umma, da samar da jagoranci na gari, dalilan da a cewarsa, suka sanya kasar shiga a dama da ita a dukkanin harkokin ci gaba na duniya.

An dai shirya makamancin wannan gangami a sassan kasar daban daban. Kuma ana sa ran gudanar da taron kungiyar ta Brics ne a birnin Durban, daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Maris mai zuwa. Inda wakilai daga kasashe mambobinta, da suka hadda da kasashen Sin, da Brazil, da Rasha, da India da kuma mai masaukin baki Afirka ta Kudu za su halarta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China