A ranar Asabar 9 ga watan nan ne aka gudanar da jana'izar wata budurwa 'yar shekaru 17 da haihuwa mai suna Anene Booysen, a Bredasdorp dake da nisan kilomota 128, daga gabashin birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, bayan da aka tsinceta jina-jina, ranar 2 gawatan nan kafin daga bisani ta rasu a wannan rana.
Masu bincike dai sun tabbatar da cewa wasu gungun mutane marasa imani ne suka yiwa budurwar fade, suka kuma sassara sassan jikinta. Tuni dai aka cafke wasu mutane 4 da ake zargin na da hannu a aukuwar wannan lamarin, ana kuma fatan gurfanar da su gaban kuliya ranar Laraba mai zuwa.
Dubban al'ummar kasar ta Afirka ta Kudu ne dai suka la'anci wannan ta'asa da ta auku, ciki hadda shugaba Jacob Zuma, wanda ya sha alwashin magance wannan matsala ta cin zarafin mata a dukkanin fadin kasar.
A wani ci gaban kuma babbar kwamishiya mai lura da harkokin kare hakkin bil'adama ta MDD Navi Pillay, ta bayyana matukar bakin ciki, don gane da faruwar wannan lamari, tana mai kira da a dauki kwararan matakan shawo kan wannan matsala ta cin zarafin mata, dake shafar dubban mata a Afirka ta Kudu, a kowace shekara.(Saminu)