Ya ce suna masu samun kwarin gwiwa dangane da ci gaba da ake samu a fuskar kawance, diplomasiya da kuma tattalin arziki tsakanin Afirka ta Kudu da sauran kasashen kungiyar BRICS.
Wannan suna na BRICS lakabi ne da ake wa kasashe masu tasowa a fuskar tattalin arziki wato, Brazil, Russia, India, Sin, da kuma Afirka ta kudu, wacce zata yi ganawarta jiko na 5 a birnin Durban daga 26 zuwa 27 ga watan Maris.
Haka zalika, shirin kawancen bunkasa nahiyar Afirka (NEPAD) da kuma shirin nazarin kawance a Afirka sunyi bukin cika shekaru 10 da kafuwa.
A matsayinsa na mai kiran taron shuwagabanni karkashin shirin NEPAD, shugaba Zuma yace Afirka ta kudu zata ci gaba da aiki da sauran kasashen don cimma aikin samar da ababan more rayuwa a nahiyar.
Dangane da batun zaman lafiya da tsaro, shugaba Zuma yace za su ci gaba da mara bayan kasar Mali a yunkurinta na tabbatar da ikon kasa.Ya kuma yi kira ga shugabannin kasashen jamhuriyar tsakiyar Afirka, Guinea Bissau, da Somaliya da su ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya don amfanin jama'arsu.
Ya yi alkawarin cewa Afirka ta Kudu zata ci gaba da mara yunkurin nahiyar Afirka a fuskar tabbatar da zaman lafiya ta hanyar shiga tsakani,ba da gudummawar dakaru da kuma tallafin na kudade da kayan aiki. (Lami Ali Mohammed)