in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncin taron harkokin zuba jari na kungiyar BRICS
2013-02-14 16:39:35 cri
Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncin taron baje koli da harkokin cinikayya na kasa da kasa da yawon shakatawa a wannan wata, gabanin taron kolin kungiyar BRICS karo na biyar.

Taken taron na kwanaki 4 wanda za a fara a ranar 21 ga watan Fabrairu a cibiyar taro ta Mmabatho da ke Mahikeng na lardin arewa maso yammaci, shi ne bunkasa harkokin cinikayya da kafofin zuba jari tsakanin kasashen BRICS da lardin arewa maso yammaci.

Thandi Modise, firaministar lardin arewa maso yammaci, wanda zai dauki bakuncin taron a madadin Pretoria, ta ce manufar taron ita ce, samar da yanayin da ya dace ga jama'a da kuma sassa masu zaman kansu, ta yadda za su amfana da harkokin cinikayya na kasa da kasa tsakanin kasashen BRICS wato Brazil, Russia, Indiya, Sin da kuma Afirka ta Kudu.

Shi dai lardin na arewa maso yammacin kasar Afirka ta Kudu, shi ne kafar tattalin arzikin kasar, saboda ayyukan hakar ma'adinai da ke gudana a wurin, aikin da ke samar da fiye da rabin abin da lardin ke samarwa tare da samar da kashi 1 bisa 4 na guraben aikin yi ga jama'ar da ke yankin.

A cewarta lardin na duba yiwuwar tattaunawa da abokan huldar kungiyar BRICS don kara karfafa hadin gwiwa a bangarorin cinikayya, yawon shakatawa da kuma zuba jari. Kimanin wakilai 300 ne ake sa ran za su halarci taron.

Kasar Afirka ta Kudu ce za ta karbi bakuncin taron kolin kungiyar kasashen BRICS da za yi a birnin Durban daga ranar 26-27 ga watan Maris.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China