in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta ci kofin Afirka
2013-02-11 16:41:43 cri
A daren ranar Lahadi 10 ga wata ne, bisa agogon wurin, aka buga wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka, a Johannesburg, babban birnin kasar Afirka ta Kudu, inda kungiyar Najeriya ta lashe takwarar ta Burkina Faso da ci 1 da nema, lamarin da ya baiwa Najeriya damar dauki kofin nahiyar ta Afirka na wannan karo.

Bayan da aka kammala wasan, jama'a masu sha'awar kwallon kafa a Najeriya sun fara bukukuwa, don taya juna murnar nasarar da kungiyarsu ta samu.

A filin wasa na Tafawa Balewa dake birnin Ikko, jama'a fiye da dubu daya sun kalli wasan ta wani babban allon telabijin, inda suka gane ma idanunsu yadda kungiyar Najeriyar wato Super Eagles, ta lashe wasan, tare kuma da kafa tarihi.

Tun dai lokacin da Najeirya ta samu maki daya kaita ga nasara a karshen wasan, jama'a ke ta ihu, da rera wakoki cikin murna. Inda bayan kammala wasan, dibban jama'a suka ci gaba da shagali a filin wasan.

A Abuja fadar mulkin kasar ta Najeriya kuwa, wasu jama'a sun kalli wasan ne a wuraren shakatawa, yayin da wasu kuma suka saurari yadda ta wakana ta rediyo.

Cin kwallon da kungiyar Najeriya ta yi ya sanya farin ciki da annashuwa a zukatan dimbin jama'ar kasar, tare da alfahari don gane da wannan gagarumar nasara.

A cewar wani mai sha'awar wasan kwallo mai suna Emmanuel, tawagar Super Eagles ta kunshi 'yan wasa matasa da yawa, wadanda suka sabunta tarihin kasar, ta hanyar kokarin lashe wannan kofi na AFCON, ya kuma yiwa kungiyar fatan kara samun nasarori a nan gaba. (Bello Wang).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China