in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana tsare da Oscar Pistorius
2013-02-14 19:52:35 cri

'Yan sanda a kasar Afirka ta Kudu sun bayyana cewa, sun tsare Oscar Pistorius, maras kafafun nan dan tseren olympics din nakasassu na Afirka ta Kudu bisa zargin kashe budurwarsa.

An bayar da rahoton cewa, Pistorius ya harbi budurwarsa mai suna Reeva Steenkamp da karamar bindiga ce da safiyar ranar Alhamis a kafada da kuma kanta a gidansa da ke Pretoria bisa zaton cewa, barawo ne.

Kakakin 'yan sanda Denise Beukes ya ce wannan batu ne na kisa, kana Pistorius wanda ya kadu saboda kashe mutum da ya yi, yana baiwa 'yan sandan hadin kai domin gudanar da bincike.

Shi dai Pitorius wanda ya daga sunan kasar, ya shiga tsere 11 a gasar da aka yi a shekara ta 2012 da kuma gasar olympics ta nakasassu, inda ya ciwo lambobin zinare biyu, da lambar azurfa kana ya kafa bajinta ta duniya sau biyu, bajinta a gasar olympics ta nakasassu da sauransu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China