in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afirka ta kudu yayi jawabi kan shirinsa a shekarar 2013
2013-02-15 16:34:46 cri
Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya sanar da shirye shiryensa na shekarar 2013 yayin jawabi na kasa ga majalisar dokokin kasar a birnin Cape Town, ranar Alhamis da maraice.

Shugaban kasar ya bayyana muhimman sassa guda biyar da gwamnatinsa zata mai da hankali kansu wato, ilmi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi, yaki da aikata laifuffuka da kuma bunkasa yankunan karkara gami da sauye sauye kan filaye.

Shugaba Zuma yafi mai da hankali ne kan ci gaba da aka samu wajen aiwatar da sabon shirin kawo bunkasa, kamar yadda yake kunshe a shirin bunkasa kasar (NDP). Wannan shiri dai an yi sanarwa kansa ne cikin watan Agustan shekarar da ta wuce inda ya bayyana dabarun shawo kan batutuwa kamar talauci, rashin daidaito da ayyukan yi.

Ya ce wannan wani tsari ne na kasar Afirka ta Kudu wanda zai tabbatar da samar da ruwa, wutar lantarki, tsabta, ayyukan yi, gidaje, ababan sufuri, abinci masu gina jiki, ilmi, kare zamantakewar al'umma,kiwon lafiya mai inganci, shakatawa da kuma tabbatar da muhalli mai tsabta.

Ana sa rai cewa ci gaban Afirka ta kudu a fuskar GDP zai kai kashi 2.5 cikin dari a wannan shekara, wato kenan zaiyi kasa da na bara wanda ya kai kashi 3.1 cikin dari.To amma kasar na bukatar samun bunkasa da ya zarce kashi 5 cikin dari domin a samar da ayyukan yi inji shugaba Zuma.

Shirin bunkasa kasar ya bayyana matakai da zasu kaiga cimma daidaito na tattalin arzikin kasar.

Shugaba Zuma ya ce ana sa ran samar da guraben aikin yi guda miliyan 11 nan da shekara ta 2030 kuma wajibi tattalin arzikin kasar ya bunkasa zuwa rubanya uku don a samar da ayyukan yi da ake bukata. (Lami Ali Mohammed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China