Jaridar ta ruwaito wadanda lamarin ya faru a kan idonsu na cewa, harin ya faru ne ranar Jumma'a a jihar Jonglei ta kasar Sudan ta Kudu da ke iyaka da Sudan.
Koda yake, gwamnan jihar Kuol Manyang ya ce, mutane 14 ne ciki har da sojoji 8 suka ji rauni, yayin da har yanzu ba a san inda gawawwakin daruruwan yara suke ba lokacin da aka kaiwa kauyen na Akobo hari.
Manyang ya ce an kai harin ne lokacin da bakin dayan mazauna kauyen ke kan hanyarsu ta shafe tsawon lokacin bazara a kan hanyar kogin Sobat.
Gwamnan ya ce, har ila, wadanda suka kai harin, sun kai samame kan wasu dabbobi, an kuma bayar da rahoton cewa, sun bazama zuwa yankin Pibor.
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su zauna cikin lumana, yana mai cewa, sojoji na kokarin gano wadanda suka kai harin. Ko da ya ke Manyang ya bayyana fargabar cewa, saboda sunkurun dajin da ke yankin da kuma nisan wurin, hakan na iya kassara kokarin sojojin na gano maharan. (Ibrahim)