Al-Bashir ya ce, zai ci gaba da yin shawarwari, da tuntubawar bangarorin daban daban na kasar, kuma ba za a kawar da yiwuwar yin shawarwari da ko wane mutum, ko dakaru dake dauke da makamai a kasar ba, musamman kokarin don warware matsalolin dake addabar kasar. Haka kuma, ya sake jaddada cewa, Sudan tana fatan kulla huldar musamman, cikin daidaito da kasar Sudan ta Kudu, haka kuma a cewarsa, kafa dangantakar sada zumunta da moriyar juna gami da samun dauwamammen ci gaba tsakanin kasashen biyu, yana da ma'anar musamman game da kiyaye zaman lafiya a wannan yanki.
A shekarar 2005, kasar Sudan da dakarun da ke adawa da gwamnati masu sansani a yankin kudancin kasar wato SPLM sun daddale yarjejeniyar zaman lafiya, don kawo karshen yakin basasa da aka shafe tsawon sama da shekaru 20 ana yi a kasar, sannan kuma aka kafa tsarin mulki na wucin gadi na shekaru 6. Tun watan Yuli na shekarar 2011, bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai, kawo yanzu, ba a samar da sabon kundin mulki a kasar ba. Yayin da babban zaben shekarar 2015 ke karatowa, akwai matukar bukatar tsara sabon kundin mulki a kasar.(Bako)