Ko da yake dai kawo yanzu, kwamitin sa ido bai gaskanta wannan lamari ba, amma an tabbatar da cewa, yanzu babu sojojin dake cikin yankunan kwance damara.
Kakakin ya jadadda cewa, ana samun kyakkyawan yanayin tsaro a iyakar kasashen biyu, bisa dalilin gudanar da yarjejeniyar tsaro tsakanin bangarorin biyu, ya kuma bayyana cewa, dole ne kasar Sudan ta Kudu ta tsayar da tuntubarta tare da 'yan tawayen kasar Sudan ta kungiyar neman 'yancin kan jama'ar kasa SPLA, wannan shi ne muhimmin mataki wajen cimma nasarar shimfida yarjejeniyar tsaro da kasashen biyu suka sanya hannu, haka shi ma ya kasance wani babban kalubale gare su. (Maryam)