Cikin wata sanarwar da kungiyar ta AU ta bayar ranar Jumma'a, shugabar hukumar gudanar da kungiyar ta lura da cewa wannan ya samar da wata sabuwar alkibla ga daidaita dangantaka tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu da kuma bude wani sabon shafi a harkar tattalin arzikin kasashen biyu, wanda ya samu koma baya matuka tun lokacin da aka dakatar da harkar man a shekarar 2012.
Ta nuna gamsuwa kan maido da kokarin hada kai da dagewa ta siyasa a bangaren kasashen biyu na inganta dangantakarsu, inda ta bukace su da su ci gaba kan wannan turba. (Lami Ali)