in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun mutu sakamakon rikicin kabilanci da ya abku a yankin Darfur dake kasar Sudan
2013-02-24 17:17:21 cri
A ranar 23 ga wata, wani rikicin kabilanci ya sake barkewa a yankin Darfur dake yammacin kasar Sudan, wanda ya haddasa mutuwar mutane 53, yayin da kuma wasu 83 suka ji raunuka.

Wasu da suka sheda abkuwar lamarin suka ce, dakarun kabilar Rizeigat da dama ne suka kai hari ga garin Al-Siraif dake jihar arewacin Darfur a ranar 23 ga wata, burinsu kuwa shi ne kai hari ga kabilar Barney Hussein. Dakarun dai sun yi amfani da manyan makamai kan kabilar da suke adawa da ita. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, mutane 53 na kabilar Barney Hussein ne suka mutu a sakamakon harin, ciki har da kananan yara 5 da mata 7. Kana mutane 83 suka samu raunuka, sa'an nan kuma aka sace tumaki fiye da dubu 40 da shanu fiye da dubu 2.

Tun daga farkon watan Janairun bana ne dai, aka fara samun rikice-rikice masu yawa tsakanin kabilar ta Rizeigat da ta Barney Hussein a garin na Al-Siraif bisa dalilan mallakar wani ma'adinin zinari, wadanda hakan ya haddasa mutuwar mutane fiye da 100, baya ga mutane dubu 130 da suka rasa gidajensu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China