Tawagar wakilan kasar Sudan sun zargi kasar Sudan ta Kudu da yi wa jerin yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka cimma a baya-bayan nan kafar ungulu. Wannan zargi ya biyo bayan wani taron tattaunawa da ya gudana tsakanin tawagar wakilan bangarorin biyu a ranar Asabar 19 ga wata a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Wata sanarwa da tawagar wakilan Sudan din ta raba wa manema labarai ta bayyana cewa, ko kusa kasar Sudan ta Kudu ba ta da niyar martaba ko aiwatar da shawarwarin da shuwagabannin kasashen biyu suka cimma, yayin zaman sulhu na baya-bayan nan da ya gabata a tsakaninsu.
Bugu da kari sanarwar ta ce, tattaunawa don gane da yankin nan na Abyei mai arzikin mai taci turane sakamakon dagewar da Sudan ta Kudu ta yi, kan a ba ta damar sanya wakilai 12, inda kuma ta bukaci Sudan ta ba da wakilai 10 domin fara tattaunawa, matakin da Sudan din ta ce sam ba ta amince da shi ba.
A ranar 7 ga watan nan ne dai kasashen biyu suka koma teburin shawara, musamman domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin na Abyei, da batun tsaron yankunan kasashen, dama daukar matakan aiwatar da ragowar yarjeniyoyin da aka cimma, aka kuma rattaba wa hannu a baya.(Tasallah)