Yayin zantawar sa da manema labaru ranar Litinin a birnin Khartoum, jim kadan bayan halartar wata tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, jagoran tawagar ta Sudan Idris Abdul-Ghader ya ce Sudan ta kudu ta yi watsi da batun killace yankin nan na "Mile 14", wanda bisa yarjejeniyar da kwamitin tsaron kungiyar AU ya jagoranta aka hana ko wane bangare jibge soji a yankin, tare da sanya tsaron sa, kan doron sharuddan da kasashen biyu suka amince da su.
Wannan dai yanki na "Mile 14" dake kan iyakar Gabashin Darfur ta Sudan, da kuma Sudan ta Kudu, na cikin muhimman yankunan da bangarorin biyu ke martabawa, kasancewar sa mai kyakkyawar kasar noma da dausayi.
Cikin watan Satumbar bara a birinin Addis Ababa na kasar Habasha ne dai, shugabannin kasashen biyu, suka rattaba hannu kan shawarwarin hadin gwiwa, da inganta tsaro, da kuma batutuwan da suka shafi warware matsaloli masu alaka da rabuwar su. (Saminu)