Sakon da kakakin Majalissar Martins Nesirky ya karanta ma manema labarai,wakiliyar hadin gwiwwa na musamman ce kuma mai shiga tsakani game da wannan batu,Aichatou Mindaoudou ta mika shi,inda ta ce wannan wani babban cigaba ne da aka samu na samar da zaman lafiya mai dorewa a Darfur,kuma tayi fatan wannan yarjejeniya zai jawo hankalin sauran kungiyoyin da ba masu saka hannu ba ne domin shiga a sulhunta dasu gaba daya.
Kasar Sudan a nata gefen wakilinta kuma shugaba mai kula da al'amurran Darfur,Amin Hassan Omer, ya sa hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da Arko Sulaiman Dahiya, mataimakin shugaban kungiyar 'yan tawaye na JEM, a wajen bikin da ya gudana a birnin Dohan.
Wannan yarjejeniya ya shimfida hanyoyin da za'a bi a fara tattaunawa a kan manyan batutuwa kamar su rabon shugabanci da arzikin kasa da kuma dawo da wadanda suka rasa matugunan su muhallin su har ma da 'yan gudun hijira.(Fatimah Inuwa Jibril)