in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bukatar lokaci wajen kafa dangantakar diplomsiyya tsakanin Iran da Masar
2013-04-15 15:23:46 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Iran Mechman Palasite ya fadi a ran 14 ga wata a birnin Tehran hedkwatar kasar cewa, ana bukatar lokaci da hakuri ne wajen kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin Iran da Masar.

Yayin da Mechman Palasite yake zantawa da manema labaru na gidan talabijin kasar Iran a wannan rana ya ce, kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu burin jama'ar kasashen biyu ne gaba daya, amma a cikin halin yanzu na rashin tabbas, ana bukatar karin lokaci da hakuri tsakanin kasashen 2. Ya ce, yanzu kasashen biyu na kokarin kyautata dangantakar dake tsakaninsu, kuma ya kamata a yi la'akari da halin da kasar Masar take ciki. Kuma ya jadadda cewa, Iran ta jima tana bayyana burinta na maido da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma babu matsala tsakanin kasashen biyu wajen kafa irin wannan dangantaka, amma halin da Masar ke ciki yanzu bai samar da yanayi mai kyau ga wannan aiki ba. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China