Michael Mann ya ce, kungiyar EU ta riga ta gabatar da sabon shirin shawarwari, kuma tana fatan Iran za ta nuna saukin kai, tare da yin rangwame game da wasu batutuwa.
Ya ce, mai yiwuwa ne, kasashe 6 da batun nukiliyar kasarta Iran ya shafa, wato Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Rasha, da Sin da kuma Jamus, za su yi shawarwari da kasar Iran, game da fasahohin nukiliya, ko da yake dai hakan ya danganta ga matsayin kasar ta Iran, da ci gaba da za a samu game da batun nukiliyar kasar.
A wannan rana, an yi shawarwari tsakanin kasar Iran da kasashe 6 da batun nukiliyar Iran ya shafa da kuma kungiyar EU a birnin Almaty, wato birni mafi girma a kasar Kazakhstan, kuma wannan shi ne karo na farko da aka koma teburin tattaunawa game da batun nukiliya na kasar ta Iran, tun bayan watanni 8 da dakatar da hakan.(Bako)