Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Wang Ming, ya bayyana matsayin da Sin ta kan dauka kan batun nukiliyar kasar Iran a ran 6 ga wata a hedkwatar majalisa dake birnin New York, inda ya ce, batun Iran na da babbar ma'ana ga tabbatar da tsarin hana yaduwar makaman nukilya da zaman lafiya da karko a yankin gabas ta tsakiya, hanya daya tilo da ta dace wajen warware wannan batu ita ce ta yin shawarwari.
Kwamitin MDD ya kira wani taro a wannan rana don sauraron rahotannin da kwamitin garkamawa kasar Iran takunkumi ya gabatar. A cikin jawabinsa, Wang Ming ya jaddada matsayin da Sin ta dauka na kin yarda da yin amfani da karfin tuwo, tare kuma da nuna rashin jin dadi dangane da kara sakawa kasar Iran takunkumi mai tsanani.
Ya ce, wasu kasashe sun dauki matakai na kashin kansu da kuma kara sanya takunkumi yadda suke so, lamarin da ya kawo barazana ga moriyar sauran kasashe, Sin kuma tana kin amincewarta kan haka ba tare da kasala ba.(Amina)