in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta kira taro a Vienna
2013-03-05 11:00:45 cri
Ran 4 ga wata, hukumar makamashin nukiliyar kasa da kasa ta kira taro a Vienna, taron da shi ne na farko da hukumar ta kira a shekarar 2013. A yayin taron, babban daraktan hukumar Yukiya Amano, ya bayyana manyan ayyukan da hukumar za ta mai da hankali a wannan shekara ta 2013.

Yayin da yake magana kan batun nukiliyar makurdadar Koriya, Yukiya Amano, ya sake yin kira ga kasar Koriya ta Arewa, da ta kiyaye yarjejeniyar hana yaduwar makamashin nukiliya daga dukkan fannoni, ya kuma nuna bakin ciki game da gwajin nukiliya karo na uku da kasar ta Koriya ta Arewa ta yi, musamman ma duba da irin kiyayyar da gamayyar kasa da kasa suka nuna ga hakan.

Amano ya kara da cewa, bayan an cimma yarjejeniyar da ke tsakanin kasashe daban daban da abin ya shafa, hukumar za ta maido da ayyukanta na binciken nukiliyar kasar Koriya ta Arewa. Haka zalika za a dauki hanyar neman warware wannan matsala cikin lumana.

Daga nan sai ya bayyana ra'ayinsa dangane da batun nukiliyar kasar Iran, yana mai ce, hukumar makamashin nukiliya za ta cigaba da yin shawarwari tare da kasar Iran, don warware matsalolin da ke ci gaba da wanzuwa. Ya kuma sake yin kira ga kasar Iran, da ta yi hadin gwiwa tare da hukumar, ta kuma ba da dama ga hukumar domin shiga cibiyar nukiliyarta dake sansanin sojan Parchin, ba tare da wani bata lokaci ba, Har ila yau Amano ya bukaci kasar Iran da ta dauki matakai a fannoni daban daban, don gudanar da manufofinta bisa ka'idojin tsaro na yarjejeniyar hana yaduwar makamashin nukiliya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China