A ranar 17 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Birtaniya William Hague ya amince da cewa, akwai hadari wajen samar da makamai ga bangaren 'yan adawa na kasar Siriya.
Yayin da Hague ke zantawa da manema labaru na kasar Birtaniya, ya ce, mai yiwuwa ne makaman da Birtaniya take samarwa masu adawa da mulkin shugaba Assad za su iyar shiga hannun masu tsattsauran ra'ayin kishin Islama na Siriya. Kuma idan rikicin ya ci gaba da tsananta, zai kawo babban hadari, 'yan ta'adda na kasa da kasa da masu tsattsauran ra'ayi za su ci gaba da tarewa a kasar Siriya, haka kuma halin rashin sanin tabbas a kasashen Lebanon, Iraqi, da Jordan zai kawo matsalar jin kai. A sa'i daya kuma, Hague ya bayyana cewa, yanzu Birtaniya ba ta yanke shawara wajen samar da makamai ga masu adawa na kasar Siriya ba.
Kwanan baya, Birtaniya da Faransa sun yunkurin neman amincewar tarayyar Turai domin ta soke takunkumin hana samar da makamai ga bangaren 'yan adawa na Siriya. Haka kuma, kwanan baya, firaministan kasar Birtaniya David Cameron ya ce, idan ba a samu ci gaba ba game da wannan batu a gun taron da za'a shirya a watan Mayu na bana, to Birtaniya za ta dauki matakinta kan wannan batu.(Bako)