Kakakin sashen ya yi bayani a wannan rana cewa, bangarorin da abin ya shafa sun riga sun shirya sosai kan sake dukkan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya guda 21 da aka tsare. Rundunar masu aikin sa ido ta riga ta aika da ma'aikatanta zuwa kauyen Jemra da wadancan ma'aikata 21 suke a daren ranar, to amma saboda yin la'akari da tsaro ne, za a gudanar da aiki a ranar 9 ga wata.
Kafin wannan, kwamitin sulhu na MDD ya yi shawarwari cikin sirri a wannan rana, inda aka saurari rahoton da mataimakin sakataren MDD dake kula da harkokin kiyaye zaman lafiya, kuma daraktan sashen kiyaye zaman lafiya, Herve Ladsous ya bayar game da sabon yanayin da ake ciki, inda ya ce, wadannan ma'aikata guda 21 suna dakunan dake karkashin wasu gidaje na kauyen Jemra inda aka tsare su, kuma suna cikin koshin lafiya.
Jami'an MDD suna kokarin neman ganin an sake su da wuri. Kasashen MDD sun bayyana baki daya cewa, za su ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin da MDD ke yi na sake ma'aikatan. (Bilkisu)