Wata kafar yada labarai ta kasar Amurka ta ruwaito maganar hukumar tsaron kasar Amurka ran 1 ga wata na cewa, na'urar Radar ta sojin ruwan kasar ta fara sa ido kan zirin Korea, musamman kan matakan soja da Korea ta Arewa ta ce za ta dauka. Ban da haka, Amurka ta tura wani jirgin ruwan yaki dake dauke da tsarin kakabo makamai masu linzami a sararin tekun zirin Korea.
Bisa labarin da gidan telibijin kasar Amurka CNN ya bayar, an ce, wannan ya kasance mataki na farko da Amurka ta dauka, kuma an bayyana cewa mai yiyuwa ne akwai jerin sauran matakai da kasar za ta kara dauka a nan gaba. (Amina)