Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Lubabatu: Ban da haka kuma, mutane masu yawon shakatawa kamar dubu 400 daga wurare dabam daban na duniya sun zo birnin Beijing a yayin da ake gudanar da wasannin Olympics. Dukkan abubuwa ya nuna cewa, wasannin Olympics na Beijing zai kasance wani babban taron wasanni wanda ke da tasiri mafi yawa ga duniya.

Lubabatu: Gasar wasannin Olympics wata dama ce mai kyau wajen nuna kasar Sin ga duniya, ita ce kuma wata damar da ke iya kusantar da Sin da duniya. Yanzu, ana lale marhabin da baki daga wurare daban daban na duniya a kasar Sin da ta yi suna a fannin nuna ladabi. Sau da yawa Mr. Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya nuna yabo ga ayyukan share fagen gasar wasannin Olympics ta Beijing, kuma yana sa fatan alheri kan samun cikakkiyar nasara a wasannin Olympics.

Bala: "Dakuna da filayen wasannin Olympics na Beijing suna da kyau sosai, a waje daya kuma ayyukan share fage na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ayyukan gayya ne, saboda haka ina sa ran alheri kan samun cikakkiyar nasara wajen wasannin Olympics."

Lubabatu: Manema labaru da yawansu ya kai sama da dubu 30, wadanda suka zo daga wurare daban daban na duniya, sun zo nan birnin Beijing don watsa labaran wasannin Olympics. Kan kokarin da kwamitin shirya wasannin Olympics na birnin Beijing ya yi a fannin ba da hidima ga kafofin watsa labaru, shugaban kwamitin daidaita harkokin gasar wasannin Olympics ta Beijing daga kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa wato Hein Verbruggen ya nuna yabo cewa, "Ba kawai babbar cibiyar watsa labaru ita ce wurin aiki na manema labaru kawai ba, har ma ita ce gidansu na biyu. Suna ayyukansu na tsawon awoyi 24 a nan, don bayar da labarai iri daban daban ga masu sauraronsu. Lallai, ya kamata mu yi godiya ga masu ayyukan shirye-shirye, saboda sun gabatar da dukkan abubuwan da manema labaru ke bukata, gaskiya ne sun sanya wurin da ya zama gidan manema labaru na dukkan duniya a cikin 'yan makoni."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13