Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Bala: A lokacin da 'yan wasan kasar Sin da suke sanye da tuffafi masu sigar Cheong-Sam, da rigar marigayi Sun Yat-sen suke shiga filin bude wasannin Olympics, kuma a lokacin da wakilan 'yan wasa na kasar Jamus masu sanye tuffafin da ke da zane zanen dodo na kasar Sin a kan su suke shiga filin bikin bude wasannin, kuma a lokacin da mai rike da tuta ta kungiyar wakilain kasar Japan Ai Fukuhara, wadda ta fahimci kasar Sin sosai, da mai rike da tuta ta kungiyar wakilai ta kasar hadaddiyar daular Larabawa gimbiya Mesa, kuma wata mace mai rike da tuta ta farko ta kasashen Larabawa, da mai rike da tutar kasar Sin ta kungiyar wakilan kasar Sin, kuma shahararren 'dan wasan kwallon kwando Yao Ming suke shiga filin, ana iya ganin cewa, dukkan 'yan wasa da ke halatar gasar wasannin Olympics suna sanar da cewa, mun shirya sosai! A madadin dukkan 'yan wasa da suke halartar gasar, Zhang Yining, 'yar wasan kwallon tebur ta kasar Sin ta yi rantsuwa cewa, Lubabatu: "A madadin dukkan 'yan wasan da ke halartar gasar zan yi rantsuwa a nan cewa, za mu tabbatar da daukakar wasannin motsa jiki da kuma girmamawar kungiyoyin wasannin, za mu shiga wasanni daban daban a fili bisa hasashen motsa jiki, kuma za mu bi ka'idojin wasannin motsa jiki da aka tsara. Kuma za mu yi kokarin shirya wata gasar da babu magungunan sa kuzari da sauran magunguna."

Bala: Wannan ne rantsuwar da 'yar wasan kwallon tebur ta kasar Sin Zhang Yining ta yi a madadin dukkan 'yan wasa.

Mr. Huang Liping , wakilin alkalan wasa ya yi rantsuwa a madadin dukkan alkalai, cewa, "A madadin dukkan alkalan wasa, da jami'ai na yi rantsuwa na tabbatar da cewa, a gun wannan wasannin Olympics, za mu sauke nauyin da ke bisa wuyanmu cikin adalci bisa ainihin hasashen motsa jiki, da girmama dukkan ka'idojin wasannin Olympics."

Bala: Wasannin Olympics na Beijing ya gabatar da wata dama ta sauraren labarin kasar Sin ga duniya. A cikin labarin, ana iya ganin wahaloli, da nasarori. Kamar daidai yadda tsohuwar 'yar wasan kwallon tebur ta kungiyar kasar Sin, kuma mataimakiyar shugaban sashen kula da harkokin kauyen wasannin Olympics na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing Deng Yaping ta ce, "Ta gasannin da 'yan wasa za su yi a wasannin Olympics, za a karfafa gwiwa ga ko wane mutum na duniya."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13