Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri
 

Lubabatu: Ban da wannan kuma, kungiyoyin wasannin fasaha suna zura idanunsu a kan dandamalin kasar Sin a lokacin wasannin Olympics. Kamfanin wasannin fasaha na kasar Sin zai nuna wasannin fasahohi na masu fasaha sama da dubu wadanda suka zo daga kasashe fiye da 30 a lokacin wasannin Olympics na Beijing.

Lubabatu: Abin da kuke saurara yanzu shi ne wasan kwaikwayon sifar babbakun Sinanci da ake nunawa a gun bikin bude gasar wasannin Olympics. Darekta Zhang Yimou yana ganin cewa, ya fi gamsuwa da wannan wasan fasaha. Kuma ya ce, "Na fi son wannan wasan kwaikwayon sifar babbakun Sinanci, wanda ya zama tamkar fasahar dab'in da ake iya sauya masa wurare ta tsoffin daulolin kasar Sin, haka kuma ya yi tamkar tafintar kwamfuta."

Lubabatu: A cikin wasan kwaikwayon sifar babbakun Sinanci, sifar bakin "He" na Sinanci ya fi jawo hankulan mutane, wanda ya nuna hasashen "Samun jituwa" da har kullum kasar Sin ke nema tun fil azal.

Bala: Fasahar kera takardu, da fasahar dab'i da kamfas, wato agogon nuna arewa, da kuma albarushi, muhimman abubuwa guda hudu ne da mutanen kasar Sin suka kirkiro a tsoffin dauloli, wadanda suka taka muhimmiyar rawa ga ci gaban zamantakewar al'ummar dan Adam. An sake nuna wadannan fasahohi hudu ta hanyar wasan fasaha a gun bikin bude gasar ne domin nuna girmamawa ga nasarorin da tsoffin daulolin kasar Sin suka samu a fannin kimiyya da fasaha bisa hasashe "shirya wasannin Olympics na kimiyya da fasaha" da aka gabatar.

Lubabatu: Wasan wuta mai kyaun gani da aka rika nunawa a sararin sama da ke kan filin wasannin Olympics na kasar Sin wato "Shekar Tsuntsu" a gun bikin bude gasar ya shaida gadon fasahar albarushi da kuma yaduwarta.

Bala: Wasan wuta na gasar wasannin Olympics ta Beijing yana da sifofin musamman, kuma an nuna shi a wuraren da fadinsu ke da yawa, wanda ya zama na farko a tarihin wasannin Olympics. Lokacin da aka kaddamar da wasannin fasaha, an nuna wasan wuta da sifarsa ta yi kamar kafaffu 29 a sararin sama da ke kan layin da ke tsakiyar birnin Beijing wato daga filin Tian'anmen na birnin Beijing zuwa "Shekar Tsuntsu", wanda ya shaida zuwan gasar wasannin Olympics ta karo na 29 a kasar Sin. Haka kuma bayan da aka kunna wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing, an nuna wasan wuta da ke da sifa iri daya a "Shekar Tsuntsu" da kuma Babbar Ganuwa da ke Juyongguan a sa'i daya, wanda ya shaida cewa, wasannin fasaha na bikin bude gasar wata hira ce da ke tsakanin gargajiya da zamani tare.

Lubabatu: Bisa kididdigar da aka yi, an ce, gaba daya ne kasar Sin ta kebe kudaden Sin wato Yuan kusan bililyan goma wajen samun nasarar kimiyya da fasaha da ke da nasaba da wasannin Olympics. Kuma bayan da aka yi kokari har shekaru fiye da shida, an samu sabbin fasahohi 625, kuma an samu dabarun aikin injiniya da sabbin kayayyaki iri 45 lokacin da ake gina ayyukan wasannin Olympics. A tarihin wasannin Olympics, wannan shi ne karo na farko da aka yi amfani da wadannan sabbin fasahohi masu dimbin yawa a sa'i daya wajen gina filaye da dakunan wasannin Olympics.

Bala: Lokacin da ake nuna wasannin fasaha a gun bikin bude gasar wasannin Olympics, 'yan sama jannati sun sauko daga sararin sama. Da zarar suka taba kasa a hankali, sai nan da nan wata samfur duniyar kasa da ke da matukar girma ta fito daga wurin da ke karkashin "Shekar Tsuntsu". An kasa wannann samfur duniyar kasa cikin zobba 9, wadda fadinta ya kai diamita 18, kum nauyinta ya kai ton 16, inda 'yan wasan kwaikwayo 58 suke tafiya a wurare daban daban. Kuma wannan ya bayyana wani hasashe, wato "muna da duniyar kasa gu daya".

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13