Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Lubabatu: Wannan ne a karo na farko da kasar Sin ta shirya gasar wasannin Olympic. Tunanin gasar wasannin Olympic ta Beijing wato 'Duniya daya, buri daya' da 'tsabtatacen wasannin Olympic da wasannin Olympic na kimiyya da fasaha da wasannin Olympic na al'adu' da kuma aniyar jama'ar kasar Sin sun jawo hankulan 'yan wasa fiye da dubu 11 daga kasashe da shiyyoyi 204 a duk fadin duniya, wannan shi ma ya alamanta cewa, yawan kasashe da shiyyoyi da 'yan wasa wadanda za su shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing zai fi yawa a tarihi.

Bala: 'Yan jarida sama da dubu 30 za su kai ziyara a a gun gasar, su ma sun fi yawa a tarihin gasar wasannin Olympic. A waje daya 'yan kallo wajen biliyan 4 za su kalli gasannin da za a shirya, adadin nan shi ma ya fi yawa a tarihin; sabbin kafofin watsa labarai kamarsu yanar gizo da wayar salula za su fara aiki a karo na farko bisa matsayinsu na hanyoyin watsa labarai masu 'yancin kai, jama'ar kasar Sin da jama'ar kasashen duniya suna begen al'ajabun da gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta kawo musu sosai da sosai.

Lubabatu: Ba ma kawai gasar wasannin Olympic wadda ake yi sau daya bayan kowane shekaru hudu ita ce wurin gasa na 'yan wasan kasashen duniya ba, har ma ita ce babban dandalin nuna al'adun kasashe daban daban na duniya. Yanzu dai ana begen bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing a yau da dare. Mene ne kasar Sin wadda ke da azurtattun al'adu masu tsawon shekaru dubu biyar za ta gaya wa duniya a gun bikin bude gasar wasannin? Game da wannan, babban diraktan bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing Zhang Yimou ya ce: "Yaya ake nuna al'adu masu tsawon shekaru dubu biyar? A takaice dai, ana iya cewa, muna son mu gaya muku cewa, 'mu wane ne' da kuma 'muna cikin iyali daya'. Bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing zai kawo wa duniya mamaki, kuma zai kawo wa jama'ar kasar Sin gamsuwa."

Bala: Taken nune-nunen wake-wake da raye-raye na bikin bude gasar wasannin Olympic shi ne "Olimpic mai kyaun gani", sun hada da sassa biyu wato su ne "wayin kai mai albarka" da "zamani mai wadata", musamman ma ana son a nuna wa jama'ar kasashen duniya dogon tarihin al'ummar kasar Sin da azurtattun al'adun kasar Sin da sakamakon da kasar Sin ta samu bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa da kuma halin ruhu da jama'ar kasar Sin ke ciki.

Lubabatu: Nune-nunen wake-wake da raye-rayen da za a yi cikin awa daya sun yi kyau da gaske kuma sun ba mu mamaki, ba ma kawai sun nuna mana halin musamman na tsoffin kasashen gabashin duniya ba, har ma sun nuna mana hali mai karfi na kasar Sin ta zamanin yau. Duk wadannan sun nuna mana fatan alheri na jama'ar kasar Sin wato jama'ar kasar Sin suna son su kafa wata duniya mai zaman jituwa tare da jama'ar kasashen duniya.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13