Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Lubabatu: Bayan da aka nuna wasannin fasaha a gun bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, shahararren mawaki na kasar Sin Mr. Liu Huan da tauraruwa mawakiya daga kasar Ingila Madam Sarah Brightman sun rera wakar babban take mai suna 'Kai da ni'. Wannan wakar da ke da dadin ji ta bayyana babban taken gasar wasannin Olympics wato 'duniya daya, mafarki daya', da ke nufin yin mu'amala da ke tsakanin kabilu da al'adu daban daban, da kara sada zumunta a tsakaninsu.

Bala: A yayin da suke rera wakar babban taken gasar, halin annashuwa ya game duk filin. Masu aikin sa kai da yawansu ya kai 2008 sun bude wata laima da ke da zane zanen fuskokin murmushi na yara na nahiyoyi biyar. A lokacin kuma, an shirya wasan wuta kamar fuskokin murmushi da yawansu ya kai 2008 a sararin sama na filin wasa na 'Shekar tsuntsu'. Game da wannan shiri, babban jagora na bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing Mr. Zhang Yimou ya gabatar da cewa, Bala: "A yayin da kake ganin wadannan fuskokin yara, za ka jiku. A ganina, fuskokin murmushi na yara da ke da launuka daban daban za su burge jama'a sosai. Sabo da muna fatan 'Yan Adam za su samu wata kyakkyawar makoma, duniyarmu za ta samu wata kyakkyawar makoma."

Lubabatu: An shirya wadannan wasannin fasaha ne har na tsawon shekaru 3 da suka gabata, mutane fiye da dubu 10 sun halarci wasannin fasaha, haka kuma manyan jagora da ke da kwarewa a duk duniya, da kungiyoyin kire-kiren fasaha, da na ba da shawarwari, a sakamakon haka ne, wasannin fasahohi masu ban sha'awa da aka nuna a gun bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing sun sa ran ko wane mutum a matsayin dawaumammun al'adun kasar Sin, haka kuma sun kasance wani shafin kide-kide masu kayatarwa a tarihin wasannin Olympics. Game da bikin bude gasar wasannin Olympics, babban jagora Mr. Zhang Yimou ya fahimce shi kamar haka,"Abubuwan da muke son bayyanawa su ne, halin kirkin 'dan Adam, da halin zuciya, da kuma kyakkyawa, wadanda suka kasance abu iri daya na duk bil Adama."

Lubabatu : 'Yan kallo da suka taki sa'a su ga wasannin fasahohi kai tsaye a gun bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing sun nuna yabo da farin ciki daga zuriyarsu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13