Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Lubabatu: Bayan babban wasan kwaikwayo na bikin budewa da aka yi, sai bikin shigo da 'yan wasa a babban filin. Mr. Liu Qi shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ya gayyaci mutane masu halartar gasar daga kasashe dabam daban daga zuciyarsa: "Shirya wata gasar Olympic mafarki ne da 'yan uwanmu Sinawa suke son cimma cikin shekaru dari 1 da suka gabata. Abun jan hankalin wasannin Olympic shi ne karfin da suke da shi na nuna juriya. Yau, mutanen kabilu daban daban da suka zo daga kasashe da yankuna 204 kuma suke bin addinai daban daban sun taru a inuwar tutar Olympic mai zobba 5 domin kokarin fahimtar juna da kara sada zumunta a tsakaninsu, kuma za su rera waka daya mai suna 'duniya daya, mafarki daya' tare. Barka da zuwa Beijing."

Bala: Ba kamar wasannin Olympics na da ba, a cikin wannan karo, 'yan wasa na kasashe dabam daban sun shiga filin wasa bisa oda ta rubutun kalmomin Sinnanci na kasashe da yankuna 204 da suke halartar gasar wasannin Olympics na Beijing. An yanke wannan shawara bayan da kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya yi jerin shawarwari tare da kwamitin wasannin Olympics na duniya, wannan yana da salon al'adun kasar Sin sosai.

Lubabatu: A ko wane karo na wasannin Olympics, kungiyar wakilan kasar Girka wadda ta zama kasa ta farko wajen shiga filin wasannin Olympics. A cikin wannan karo, launin tufaffin kungiyar wakilan kasar Girka shi ne fari da toka-toka kadan. Wanda ya kago wannan tufafi ya ce, yana fatan kungiyar wakilan kasar Girka za ta iya kawo wa mutane farin ciki da haske, da kuma yada labarin zaman lafiya, da abokantaka, da kuma hadin kai.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13