Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Bala: Mr. Rogge shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya ya ce, motsa jiki ya iya kafa gadon mu'amala a tsakanin jama'a, kuma ya sanya 'yan Adam su sami buri na zaman lafiya da jituwa tare. Ya ce, "Ko wane irin zaman al'umma, da al'adu, da harshe, da tsarin mulki, da addini, membobi 205 na kwamitin wasannin Olympics na duniya suna zaman tare cikin lumana, wannan yana da muhimmanci sosai ga hadin kan 'yan Adam."

Lubabatu: Ban da 'yan wasa da yawa da ke halartar bikin bude wasannin Olympics na Beijing, akwai shugabanni ko manyan jami'ai fiye da 80 na kasa da kasa sun halarci wannan biki, yawansu ya sabunta bajintar tarihin wasannin Olympics. Wadannan shugabanni ko manyan jami'ai sun kunshi shugaba Bush na kasar Amurka, da firaminista Yasuo Fukuda na kasar Japan, da shugaba Shimon Peres na kasar Isra'ila, da shugaba Nursultan Nazarbayev na kasar Kazakhstan, da firaminista Kevin Michael Rudd na kasar Australia da dai sauransu.

Bala: Tsohon abokin jama'ar kasar Sin Mr. Samaranch shugaban girmamawa na kwamitin wasannin Olympics na duniya wanda ya kai shekaru 88 da haihuwa ya halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ya ce, "Ina farin ciki saboda na iya halartar bikin kaddamar da gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008. Na san yadda jama'ar kasar Sin ke allah-allah wajen gudanar da wasannin Olympics, da yawan kokarin da suka yi domin gudanar da wasannin Olympics na wannan karo. Na yi imanin cewa, wasannin Olympics na wannan karo zai sami nasara kuma zai zama mai walkiya, kuma mai yiyuwa ne zai zama wani karo mafi kyau a tarihin wasannin Olympics. Dukkan abubuwan da na gani a Beijing sun dace da burina kafin shekaru 7."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13