Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Lubabatu: A gun gagarumin bikin kaddamar da gasar da aka yi sa'o'i 3 da rabi ana yinsa, abin da ya fi jawo hankulan mutane shi ne, lokacin da aka kunna wutar wasannin Olympic. Bayan da aka yi kwanaki 133 ana mika wutar a duk fadin duniya da tsawon hanyar mika wutar ya kai kimanin dubu daruruwa, daga karshe dai an isar da wutar a wannan filin wasannin motsa jiki na kasar Sin, wato "Shekar Tsuntsu". Sabo da haka 'yan kallo fiye da dubu 90 suna da annushuwa sosai lokacin da suke kallon isowar wutar.

Lubabatu: A karkashin zura ido da dukkan 'yan kallo suka yi, Mr. Li Ning, tsohon mashahurin dan wasan lankwashe jiki na kasar Sin ya karbi wutar wasannin Olympic a matsayin mai rike wutar na karshe. Da ya samu wutar, ya tashi daga kasa zuwa rufin filin wasannin motsa jiki na kasar Sin, wato "Shekar Tsuntsu" ya soma gudu. Da ake kallonsa, yana gudu a kan wata hanyar da ke sararin sama. Lokacin da yake gudu, sannu a hankali ne aka bude wani zane na sifar Sin. A kan wannan zane, an bayyana yadda aka mika wutar tun daga birnin Athen na kasar Girka zuwa birnin Beijing a duk fadin duniya. Bayan da aka bude wannan zane duka, ya nadi da kansa kuma ya zama babbar wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing. Sannan kuma, Li Ning ya kunna wani layi, wannan layi ya tashi sannu a hankali har ya kunna babbar wutar yola. Wuta ta ci a cikin babbar yola. Wannan ne karo na farko da aka hada aikin mika wutar da aka yi a duk fadin duniya da aikin kunna babbar wutar yola da kyau kamar haka.

Bala: An isar da wannan wutar da ke dauke da alfahari da mafarki da fatan alheri da kuma makomar da ake nema, kuma aka dauke ta a garin wasannin Olympic a wannan ranar da aka bude gasar Olympic ta karo na 29. Da karfe 12 da minti 4 na ran 8 ga watan Agusta da dare na shekarar 2008, an kunna babbar wutar yola da wannan wuta mai tsarki. A wannan lokaci, dukkan 'yan kallon da ke cikin "Shekar Tsuntsu" suna ta ihu, duk kasar Sin, har ma duk duniyarmu suna cike da jikuwa sosai.

Lubabatu: Kunna wuta a gun babbar wutar yola ta fi jawo hankulan mutane a gun dukkan gasannin Olympic da aka yi. Muna mamaki sosai ga bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing wadda ke cike da al'adun gargajiya na kasar Sin, kuma ke cike da fasahohin zamani.

Bala: A gun dukkan gasannin Olympic da aka taba shiryawa a da, hanyar kunna babbar wutar yola ta gasar Olympic ta kan jawo hankulan mutane sabo da a kan mai da hankali sosai wajen kirkiro sabuwar hanyar kunna ta.

Lubabatu: Jama'a masu sauraro, ma'anar wutar wasannin Olympic da aikin mika ta ba sanar da budewar gasar Olympic kawai ba, har ma ta kan bayyana ruhun Olympic, kuma ta kan alamantar da karfin hada kan bil Adam na duk duniya da yin musanye-musanye a tsakanin al'adu iri daban daban.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13