Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Bala: Wasan fasaha na farko da aka nuna a gun bikin bude wasannin Olympics na Beijing shi ne makada 2008 wadanda ke saye da tufafin gargajiya sun kada kayan kida da ake kira "Fou" tare. Abin da ake kira "Fou" shi ne wani irin kayan kida na gargajiya na kasar Sin, wanda ke da tsawon tarihi na shekaru kusan 3000.

Lubabatu: Yayin da ake kada "Fou", a kan babban allon da ke wurin, an kuma nuna shahararrun kalmomin Confucius, wato wani mashahurin masanin falsafa a zamanin gargajiyar kasar Sin, kuma kalmomin suna cewa, "abin farin ciki ne a samu zuwan aminai daga wurare masu nisa", don nuna maraba ga aminai daga kasashen duniya, wanda kuma ya kasance manufar bikin bude wasannin Olympics na Beijing.

Bala: A gun bikin bude wasannin Olympics na Beijing, an yi amfani da abubuwa da dama da ke shafar al'adun kasar Sin, musamman ma wani babban zanen da ke da tsawon mita 20 da fadin mita 11, wanda kuma nauyinsa ya kai kilogram 800. Ban da wannan kuma, an sanya alamu masu yawa na al'adun kasar Sin, ciki har da maficicin gargajiya na kasar Sin da rubuce-rubucen da aka yi da brush da sassaka da aka yi a kan gora da filfili da dai sauransu.

Lubabatu: Wannan bikin da ke cike da al'adun kasar Sin ya burge 'yan kallo sosai. Wakilin wani gidan telebijin na Mexico, wanda ya kalli gwajin bikin bude wasannin Olympics, ya ce wasannin fasaha da aka nuna sun bayyana ainihin al'adun kasar Sin.

Bala: "Wasannin fasaha da aka nuna a gun bikin sun bayyana al'adun kasar Sin sosai, ko da yake wani kashi ne kawai na al'adun kasar Sin, amma ya bayyana ainihin al'adun kasar Sin, wato zaman jituwa da juna da girmama juna."

Lubabatu: Ba ma kawai bikin bude wasannin Olympics ba, hakika kullum ana bayyana manufar "wasannin Olympics da ke da nagartattun al'adu" a duk lokacin da ake share fagen wasannin Olympics. Tun daga shekarar 2003, bi da bi ne aka kaddamar da jerin alamun wasannin Olympics na Beijing, wadanda ke bayyana al'adun kasar Sin sosai, ciki har da tambarin wasannin Olympics na Beijing da yara biyar masu fatan alheri da ake kira "Fuwa". A game da yara 5 masu fatan alheri, Mr.Shui Tianzhong, mashahurin mai sharhin fasahohi na kasar Sin ya ce, "Yara 5 masu fatan alheri da muka kaddamar, alamu ne na zumunci da kuzari, wadanda ba ma kawai suka sanya wa al'adunmu sabuwar ma'ana , haka kuma sun kara wa wasannin Olympics sabuwar al'ada."

Lubabatu: Wasannin Olympics ba ma kawai dandali ne na nuna al'adun kasar Sin, haka kuma biki ne na al'adun kasashe daban daban na duniya. A karo na farko ne kwamitin wasannin Olympics na duniya ya ba da shawarar gudanar da bikin baje kolin Olympic a nan birnin Beijing, inda za a nuna wasu kayayyaki masu daraja da aka kawo su daga gidan nune-nunen kayayyakin wasannin Olympics da ke birnin Lausanne na kasar Switzerland. Mr.Zhao Dongming, shugaban sashen kula da al'adu na kwamitin wasannin Olympics na Beijing, yana ganin cewa, wannan ya bayyana manufar wasannin Olympics na cudanyar al'adu iri daban daban.

Bala: "Muna kokarin neman hada yanayin kasar Sin da ka'idojin duniya gu daya, wato ba ma kawai mu nuna dadadden tarihi da al'adu na kasar Sin kawai ba, haka kuma muna son bayyana cudanyar al'adu iri daban daban ta hanyar sa hannayen kasashen duniya a ciki."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13