Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Lubabatu: A karo na farko ne aka daga tutar kasar Sin mai dauke da taurari biyar a gun bikin bude gasar wasannin Olympic, mawaka 224 daga kabilu 56 na kasar Sin sun rera taken kasar Sin da babbar murya tare don nuna wa jama'ar kasashen duniya farin ciki da alfaharin da jama'ar kasar Sin ke ji a wannan lokaci.

Bala: A gun bikin, shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya Jacques Rogge ya nuna fatan alherinsa inda ya darajanta kokarin da kasar Sin ke yi domin wasannin Olympic sosai. Mr. Rogge ya ce, "Kasar Sin ta dade tana da mafarki na bude kofarta ga kasashen duniya da na gayyatar 'yan wasa na yankuna daban daban da su zo birnin Beijing domin halartar gasar wasannin Olympic. Yau da dare, mafarki ya zama gaskiya. Taya Beijing murna! Lokacin da muke cimma burinmu na Olympic, a cikin sahihanci ne muka gode wa kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing. Mun gode musu sabo da kokarin da suka bayar. A waje daya kuma, mun gode wa dubban mutane masu aikin sa kai. Idan babu kokarin da suka bayar, da ba za mu iya cimma burinmu ba."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13