Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Bala: Tun daga ran 1 ga watan Afrilu zuwa ran 3 ga watan Mayu, an mika wutar gasar Olympic ta Beijing a birane 19 da suke wakiltar al'adu iri daban daban da ke fadin duk duniya. A birnin Dares Salam na kasar Tanzaniya, dimbin mutane sun fita tituna sun yi ihu a kan hanyar mika wutar da tsawonta ya kai kilomita 5 kawai. Mr. Qu Yingpu, kakakin kungiyar mika wutar ta kwamitin shirya gasar Olympic ta Beijing ya tuna da cewa, "Ya kasance da wasu ramukan ruwa kanana da manya. Tayoyin motocinmu ma sun shiga wadannan ramukan ruwa. Na ga yara da yawa sun cire takalma da socinsu da farko sun wuce wadannan ramukan ruwa, sannan sun sake sanya takalma da soci sun ci gaba da bin sawun wutar. Jama'ar Afirka sun burge mu a cikin zukatanmu."

Lubabatu: Ko lokacin da aka gamu da matsala kuma aka lalata aikin mika wutar a wasu biranen kasashen duniya, mutane da yawa suna sa kaimi ga wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic ta Beijing. Mr. Peter V. Ueberroth ya nuna cewa, "Ya kamata a girmama wutar wasannin Olympic, kuma ya kamata a girmama masu rike da wutar."

Bala: A cikin zukatan masu rike da wutar, sun nuna bakin jininsu sosai ga laifin keta da tsoma baki kan aikin mika wutar. Mr. Todd Lincoln, mai shekaru 46 da haihuwa, wani likitan kasar Amurka wanda ya mika wutar wasannin Olympic ta Beijing a birnin San Fransisco ya ce, "Kowa na da 'yancin bayyana ra'ayinsa, amma idan an keta ko hana sauran mutane da su bayyana ra'ayoyinsu, wannan laifi ne da ba za a iya amincewa da shi ba."

Lubabatu: Zobba 5 na Olympic suna kyalkyali, wutar wasannin Olympic tana ci. An riga an bude gasar Olympic ta Beijing. A cikin kwanaki 16 masu zuwa, 'yan wasa da suka zo daga nahiyoyi 5 na duk duniya za su yi amfani da makinsu domin bayyana ruhun Olympic, wato "mafi sauri da mafi kyau da kuma mafi karfi" da tunanin "halarta ya fi samun nasara muhimmanci", wato ainihin ruhun Olympic.

Bala: Ana da imani cewa, a karkashin tutar Olympic mai zobba 5, za a samun sabon cigaba a gun gasar Olympic ta Beijing a cikin tarihin wasannin Olympic, kuma za a bude sabon shafi na tabbatar da zaman lafiya da sada zumunci da neman samun cigaba.

Lubabatu: To, jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen duk shirinmu na musamman game da bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing. Mun gode muku kwarai da gaske sabo da kuna kasancewa tare da mu a cikin wadannan mintoci kusan hamsin. Muna fatan za ku ji dadin shirye-shiryenmu game da gasar Olympic ta Beijing a cikin kwanaki 16 masu zuwa. Ni Lubabatu da Alhaji Balarabe shehu Ilelah ke muku godiya a madadin Sani Wang da Umaru da Sanusi da Jamila da Bilkisu da Kande da Musa da Danladi, kuma ke cewa ku kasance lafiya.


1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13