Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:26:21    
An soma gasar Olympic ta Beijing

cri

Bala: Gidan Rediyon kasar Sin! ni ne Balarabe Shehu Ilelah. Yanzu, ni da Lubabatu za mu gabatar muku wani shirin musamman game da bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing.

Lubabatu: Barka da wannan lokaci. Dazun nan kun saurari wata waka mai dadin ji kuma mai suna: "Wakar gasar wasannin Olympic". Yau, wato ran 8 ga wata da dare, agogon Beijing, aka rera wannan waka a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, wannan ya alamanta cewa, an riga an bude zama ta 29 ta gasar wasannin Olympic ta yanayin zafi!

Bala: Wannan rana da dare, dukkan jama'ar birnin Beijing da jama'ar kasar Sin suna jin dadin gaggarumin bikin nan tare. 'Yan wasa sama da dubu 11 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 205 suna taruwa a karkashin Tutar Olympic mai zobba 5 a gun bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, da haka, babban iyalan Olympic ya sake taruwa a tarihinsa.

Lubabatu: Wannan shi ne muhimmin bikin da jama'ar kasar Sin suke begensa sosai da sosai, kuma ya jawo hankulan kasashe daban daban a duk fadin duniya.

Bala: A gun bikin bude gasar, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya sanar da cewa, "Yanzu, na sanar da cewa, gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta Beijing ta soma!"

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13