logo

HAUSA

Xi Jinping ya aika sakon taya murna ga Taneti Maamau bisa sake zabensa a matsayin shugaban Kiribati

2024-10-27 19:15:42 CMG Hausa

Yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga Taneti Maamau, don taya shi murnar sake zabensa da aka yi a matsayin shugaban jamhuriyar Kiribati, inda ya kuma bayyana fatansa na yin aiki tare da shugaba Maamau, don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Bilkisu Xin)