logo

HAUSA

Hanyoyin zaman rayuwa masu dacewa na taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da cutar damuwa

2024-10-24 07:13:21 CMG Hausa

 

Wani sabon nazari ya gano cewa, hanyoyin zaman rayuwa masu dacewa guda 7, wadanda suka hada da cin abinci yadda ya kamata, da motsa jiki kullum, suna taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da cutar damuwa sosai.

Masu nazarin da suka fito daga jami’ar Fudan ta kasar Sin, da jami’ar Cambridge ta kasar Birtaniya, sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanan baya cewa, sun bibiyi mutane kusan dubu 290 da aka tanada cikin rumbun adana bayanai masu alaka da likitanci, da halittu na kasar Birtaniya, kuma sun gano cewa, akwai hanyoyin zaman rayuwa guda 7 masu nasaba da raguwar barazanar kamuwa da cutar damuwa.

Alal misali, yin barci ta hanyar da ta dacewa, wato daukar awoyi 7 zuwa 9 a kowane dare ana barci, ya fi yin tasiri kan raguwar barazanar kamuwa da cutar damuwa, da har kashi 22 cikin kashi 100. Sa’an nan rashin shan taba, da yin mu’amala da mutane kullum, da motsa jiki lokaci zuwa lokaci, da rashin yawan zama a wuri guda, da rage shan giya, da cin abinci masu dacewa su 6, suna rage barazanar kamuwa da cutar damuwa da kashi har 20 cikin 100, da kashi 18 cikin kashi 100, da kashi 14 cikin kashi 100, da kashi 13 cikin kashi 100, da kashi 11 cikin kashi 100, da kashi 6 cikin kashi 100 bi da bi.

Masu nazarin sun raba masu shiga nazarinsu zuwa rukunoni guda 3, bisa hanyoyin da masu shiga nazarin suke kai. Idan an kwatanta su da wadanda ba sa rayuwa ta hanyar da ta dace, barazanar da wadanda suke bin managartan hanyoyin zaman rayuwa suke fuskanta wajen kamuwa da cutar damuwa, ta kan ragu da kashi 57 cikin kashi 100, yayin da barazanar da wadanda suke rayuwa kan matsakaitan hanyoyi suke fuskanta ta ragu da kashi 41 cikin kashi 100.

Har ila yau, masu nazarin sun gano cewa, barazanar kamuwa da cutar damuwa, tana da nasaba da kwayoyin halitta na gado, amma duk da haka yin rayuwa ta hanyoyi masu dacewa, ta fi ba da tasiri kan raguwar barazanar.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, likita dake aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi mana karin bayani da cewa, duk da kasancewar kwayoyin halitta na gado, da rayuwa ta hanyoyi masu dacewa yana taimaka wajen rage barazanar kamuwa da cutar damuwa, a hannu guda yin rayuwa ta hanyar da ba ta dace ba, yana kawo illa ga tsarin garkuwar jikin dan Adam, da kuma yadda ake sarrafa sinadarai a jikin dan Adam, ta yadda za a kara barazanar kamuwa da cutar ta damuwa. (Tasallah Yuan)