Bakin ciki yana da amfani ga dan Adam
2024-10-14 15:51:44 CMG Hausa
Hadaddiyar kungiyar masu nazarin tunanin dan Adam ta kasar Amurka ta kaddamar da rahoto a kwanan baya cewa, ko da yake a kan mayar da fushi a matsayin wani nau’in na rashin jin dadi ko mara yakini, yana iya karfafa gwiwar mutane su daidaita kalubale a zaman rayuwarsu.
Masana ilmin tunanin dan Adam sun yi nuni da cewa, har kullum mutane suna fatan yin farin ciki. Galibin mutane suna neman yin farin ciki a duk tsawon rayuwarsu. Idan wasu suna cikin koshin lafiyar tunani, kana suna farin ciki, su kan kasance cikin yanayi na jin dadi da yakini. Amma rashin jin dadi, kamar yin fushi da sauransu, yana haifar da tasiri mai kyau.
Masu ilmin amfanin tunanin dan Adam suna ganin cewa, dukkan wani yanayi na farin ciki ko akasinsa, martani ne da a kan mayar kan halin da ake ciki, da nufin yin gargadi kan muhimman batutuwan da wajibi ne a dauki matakai wajen daidaita su. Alal misali, idan wani yana cikin bakin ciki, to, mai yiwuwa yana bukatar a tallafa masa ko a ba shi goyon baya. Idan wani yana fushi, to, watakila yana bukatar daukar matakai don daidaita matsaloli.
Da nufin kara sanin amfanin yin fushi wajen cimma buri, masu nazari sun gudanar da gwaje-gwaje, wadanda suka shafi mutane fiye da dubu 1, tare da tantance bayanan masu amsa tambaya fiye da dubu 1 da dari 4. A cikin kowane gwajin, masu nazarin sun sanya masu shiga gwajin sun yi fushi ko farin ciki, sa’an nan sun gabatar musu manufa mai wuyar cimmawa.
A cikin dukkan gwaje-gwajen, a cikin kowane hali, yin fushi ya kyautata karfin mutane na cimma manufofi masu wuyar cimmawa.
Masu nazarin sun bayyana cewa, sakamakon gwaje-gwajen ya nuna cewa, yin fushi yana kyautata kokarin mutane na cimma wata manufa, lamarin da zai taimaka wa mutane samun babbar nasara, wadda ta wuce zatonsu.
Sun ci gaba da cewa, yin fushi kan karfafa gwiwar mutane su nemi cimma manufofi masu wuyar cimmawa, yayin da ba ya amfani sosai wajen cimma manufofi masu saukin cimmawa. Ga alama, yin fushi, kasancewa cikin halin kunci, ko bakin ciki, wadanda ake daukarsu a matsayin yanayin mara yakini, suna amfamawa mutane wajen cimma manufofi. (Tasallah Yuan)