logo

HAUSA

An juya bangare na karshe na gadar titi mafi tsawo dake saman layin dogo a kasar Sin

2024-10-27 16:36:48 CMG Hausa

An kammala juya bangare na karshe na gadar titi mafi tsawo dake saman layin dogo zuwa gurbinsa, a birnin Hefei na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin da sanyin safiyar jiya Asabar.

Gadar mai tsawon mita 554 da nauyin ton 60,000 ta hada sassa 4 da tsawonsu ya kai layin dogon dake kasan titin, wadanda aka kammala juya uku daga cikinsu a karshen watan Satumba.

Gadar mai sassa da dama, wani bangare ne na babbar hanyar da ta ratsa larduna, ta hada birnin Chuzhou na lardin Anhui da Zhoukou na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin. Nasarar juya bangare na karshe na titin ya kawo aikin babbar hanyar dab da kammaluwa.

Ana sa ran hanyar za ta karfafa hada birnin Hefei da manyan biranen gabashi da tsakiyar kasar Sin, ciki har da Nanjing da Hangzhou da Zhengzhou. Hadewar biranen na da muhimmanci matuka domin za ta tallafa wajen gaggauta shigar da Hefei cikin aikin raya yankin kogin Yangtze. (Fa’iza Mustapha)