logo

HAUSA

Adadin kamfanonin kula da jirage marasa matuka ya zarce dubu 17 a kasar Sin

2024-10-26 16:21:20 CMG Hausa

Yayin da ake ci gaba da gudanar da dandalolin tattaunawa, karkashin babban taron zirga-zirgar jiragen sama, na kungiyar zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin wato CATA karo na biyu, an gabatar da wasu rahotanni 2, da suka hada da na ci gaban zirga-zirgar jiragen saman kasar Sin, gami da na ci gaban zirga-zirgar jiragen sama marasa matuka na amfanin jama’ar kasar Sin a daya daga dandalolin.

Rahotannin biyu sun shaida cewa, sakamakon habakar tattalin arzikin kasar Sin, kasuwar zirga-zirgar jiragen sama ta fadada, tare da kara samun karfin ci gaba, musamman ta fannin amfani da jirage marasa matuka.

A shekara ta 2023, tsawon lokacin zirga-zirgar jiragen saman da aka saba amfani da su na kasar Sin, ya kai awa miliyan 1.371, adadin da ya karu da kaso 12.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara. Zuwa watan Yulin shekarar da muke ciki, yawan kamfanonin kula da harkokin jiragen sama ya kai 712 a duk fadin kasar Sin. Kana, a ’yan shekarun nan, karuwar tattalin arzikin da ya shafi sana’o’in zirga-zirgar jiragen sama marasa matuka a kowace shekara a kasar Sin, ta zarce ta zirga-zirgar jiragen saman da aka saba da su, da kaso 10 bisa dari, al’amarin da ya kasance babban karfi da ke jagorantar ci gaban tattalin arzikin, mai nasaba da jiragen sama, ko na’urorin dake zirga-zirga a kusa da doron kasa.

Kaza lika, kawo yanzu, adadin kamfanoni masu kula da zirga-zirgar jiragen sama marasa matuka a kasar Sin ya wuce dubu 17, kana, yawan jirage marasa matuka da jama’a suka yi rajista ya zarce miliyan 2.

Bugu da kari, kasar Sin ta dade da zama babbar kasa dake kan gaba a duniya, ta fannin fitar da jiragen sama marasa matuka na amfanin jama’a zuwa kasashen waje. Kaza lika, yawan ikon mallakar ilimin da ya shafi bangaren jiragen sama marasa matuka da aka nema a kasar Sin, ya dauki kaso 70 bisa dari a duk duniya, al’amarin da ya sa kasar ta zama wadda ke kan gaba a duniya, wajen fitar da fasahohin da suka shafi wannan fanni. (Murtala Zhang)