logo

HAUSA

Nijar na cikin juyayin mutuwar Hama Amadou tsohon faraminista kuma tsohon shugaban majalisar dokoki

2024-10-25 09:59:32 CMG Hausa

 

A cikin daren ranar Laraba 23 zuwa Alhamis 24 ga watan Oktoban shekarar 2024, Allah ya yi tsohon shugaban majalisar dokokin Nijar Hama Amadou rasuwa a lokacin da yake da shekaru 74 da haihuwa, bayan ya yi fama da rashin lafiya. A yau juma’a 25 ga watan Oktoban shekarar 2024 aka yi bikin girmama mamacin a fadar shugaban kasa, kafin a dauki gawarsa zuwa kauyen Youri inda za’a jana’izarsa.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada, ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

Tun lokacin da labarin mutuwarsa ya bazu a cikin kasa da ma duniya baki daya, ’yan Nijar maza da mata suka fara juyayin mutuwar wannan gawurtaccen dan siyasa, wanda ya sha gwagwarmaya domin ’yancin kasar Nijar, da tabbatar da tsarin demokaradiyya na-gari.

A tsawon rayuwarsa Hama Amadou, ya kasance dan siyasa da ake sauna, da ba ya ja da baya kan gaskiya. Ginshikin dan siyasar Nijar tun lokacin shugaba Seyni Kountche zuwa shugaba Tandja Mamadou, Hama Amadou ya rike manyan mukamai da suka hada da kasancewa faraminista a shekarar 1995, kana shugaban majalisar dokoki duk a lokacin mulkin shugaban kasa Tandja Mamadou. Bayan ficewa daga jam’iyyar MNSD-Nasara, Hama Amadou ya kafa jam’iyyarsa ta Modem FA Lumana Afrika.

An haifi Hama Amadou a ranar 3 ga watan Maris din shekarar 1950 a kauyen Youri, yankin Tillabery. Kuma ya bar duniya a lokacin da yake da shekara 74 da haihuwa.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.