logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin habaka hadin gwiwar BRICS nan gaba

2024-10-24 15:31:17 CMG Hausa

 

An cimma nasarar gudanar da taron ganawar shugabannin BRICS karo na 16 a Kazan na kasar Rasha a jiya Laraba. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, inda ya nanata wajibcin raya BRICS da ta zama wani muhimmin dandali na karawa kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwar kwarin gwiwar hadin kansu da kuma zama ingantaccen karfin ingiza daidaita harkokin duniya, kuma ba da shawarwari ga mabambantan bangarori da su raya tsarin BRICS tare a bangaren zaman lafiya da kirkire-kirkire da kiyaye muhalli da habaka al’adu bisa adalci, tare kuma da sanar da jerin hakikanin matakai, abin da ya jawo hankalin kasa da kasa.

Shugaban sashen nazarin nahiyar Asiya da Turai na kwalejin nazarin huldar kasa da kasa na kasar Sin Ding Xiaoxing ya yi tsokaci cewa, jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi na samar da wata akida da hanyar da suka fi dacewa na hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kuma ya bayyana karfin jagorancin Sin a ko da yaushe, hakan kuma ya samar da tsari iri na kasar Sin wajen gaggauta inganta hadin gwiwar BRICS+.

Idan mun leka ci gaban da aka samu a yayin taron, shawarar da Sin ta gabatar mai taken “Manyan bangarori biyu na BRICS” ya mai da hankali a fannin tsaro, bunkasuwa da daidaita harkokin duniya da mu’ammalar al’adu da sauransu, wanda ya hada shawarwari da Sin ta gabatar tare da dabarar bunkasuwarta da muradun BRICS da ma fatan al’ummar duniya zuwa waje guda, hakan zai amfanawa kasashen BRICS da su samu bunkasuwa ta dogaro da kai, kuma da amsa tambayoyin da ake yiwa BRICS game da hadin gwiwarsu.

Idan aka yi hangen nesa, a wannan sabon yanayi na samun madogarai da dama a duniya da rikicin sabon yakin cacar baka, ya kamata kasashen BRICS su amince da mabanbantan ra’ayoyi tare da kokarin hadin gwiwarsu, ta yadda za a bude wani sabon yanayi na samun karin ingantaccen bunkasuwa bisa tsarin BRICS+, wanda zai ba da jagoranci ga raya kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwa, har ya zama karfin raya kyakkyawar duniya mai inganci. (Amina Xu)