logo

HAUSA

Kasar Sin: Tsohuwar Kasa, Mai Jagorantar Zamanantar Da Duniya

2024-10-22 20:10:20 CMG Hausa

Duk inda aka ambaci sunan kasar Sin, to kowa ya san cewa tsohuwar kasa ce mai dadadden tarihi da tarin al'adun gargajiya. Sai dai duk da haka, kasa ce mai tafiya da zamani. Muna ma iya kiranta da jagora a fannin zamanantar da duniya. Kaso mai yawa na kayayyakin zamani da ake amfani da su yanzu, sun samo asali ne daga kasar Sin, saboda ingantattun fasahohin da take da su kuma take ci gaba da kirkirowa.

Kamar yadda Mallam Bahaushe kan ce "noma tushen arziki". To haka batun yake a wajen kasar Sin. Daya daga cikin muhimman abubuwan da dan adam ke bukata shi ne abinci. Kuma bisa la'akari da yawan al'ummar kasar Sin, har kullum yadda take iya dogoro da kanta da kuma kokarinta na ciyar da daukacin al'ummarta, abun al'ajabi ne, wanda ke matukar jan hankalina.

Daya daga cikin sirrikan kasar Sin na samun ci gaban ayyukan gona shi ne yadda take amfani da fasahohin zamani wajen zamanantar da ayyukan.

A yau yayin da nake ziyara a birnin Harbin na lardin Heilongjiang ta arewa maso gabashin kasar Sin, na ziyarci wata gonar masara yayin da ake gudanar da aikin girbi, inda na ga yadda injuna ke aiki cikin aminci fiye da zatona. A lokaci guda, injin kan yanke karar masara, ya fidda ganyayyaki ya kuma casheta. Cikin kankanin lokaci yake gudanar da aikin da zai dauki dimbin lokaci, wanda zai bukaci ma'aikata da karfi da kuma kudi mai yawa. Haka kuma a rana guda, motar ko inji za ta iya girbe gona mai fadin murabba'in mita dubu 667, kwatankwacin awon Sin mu 1000 a rana guda.

Ban da haka kuma, a rana guda za a yi amfani da injuna wajen kara gyara masarar, kama daga cire ragowar totuwa da sanduna, zuwa cire dusa da kuma busarwa, duk injuna ne ke aiwatar da wadannan ayyuka cikin lokaci kankani.

Ba girbi kadai ba, hatta gyaran gonaki da shuka da feshi da kula da shuke-shuke, duk injuna ne ke gudanar da su.

A yau na kara tabbatar da cewa kasashe masu tasowa mussamam namu na Afrika da har yanzu muke fama da matsalar karancin abinci da rashin ci gaba a fannin aikin gona, na da dimbin abubuwan koyo daga kasar Sin.

Sai al'umma ta koshi kafin za ta kasance mai lafiya da karfin nema da tsaro da kwanciyar hankali da kuma uwa-uba ci gaba. Wannan, daya ne daga cikin sirrikan Sin na samun ci gaba. (Faeza Mustapha)