logo

HAUSA

Wadanne sakamako aka samu daga cinikin tsakanin Sin da kasashen ketare

2024-10-16 15:17:13 CMG Hausa

Kwanan nan an fitar da sabbin alkaluman ciniki tsakanin Sin da kasashen waje, kuma abin lura shi ne, a farkon watanni 9 na bana, a karo na farko, kudin hajojin da kasar Sin ta fitar da su kasashen waje da ma shigo da su daga ketare ya zarce kudin Sin yuan triliyan 32, adadin da ya kai triliyan 30.8 a makamancin lokacin a bara. Ban da haka, a kowane rubu’i na wannan shekara, adadin ya zarce yuan triliyan 10, wanda kuma ya kasance na farko a makamancin lokacin a shekarun baya.

A yayin da ake fuskantar karin matakan kariyar ciniki da wasu kasashe suka dauka da ma yadda tattalin arzikin duniya ke farfadowa, yadda kasar Sin ta tabbatar da karuwar ciniki tsakaninta da kasashen ketare fiye da yadda aka yi hasashe, ba abu mai sauki ba ne.

In mun yi la’akari da yanayin ciniki a cikin gidan kasar, hajojin da kasar Sin ta samar suna da karfin takara sakamakon yadda ake samun cikakken tsarin samar da kayayyaki da saurin ci gaban fasahohi a kasar, matakin da ya aza tushen rika fadada kasuwanninsu a duniya.

Sai kuma in mun duba yanayin ketare, yadda bukatun kasuwannin ketare suka farfado ya samar da kyawawan sharuda ga kasar wajen fitar da kayayyakinta zuwa gare su. Rahoton da kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO ta fitar a kwanan baya ya kyautata hasashenta kan yawan cinikin hajojin na duniya cikin shekarar bana.

Ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen ketare ya kuma samar wa kasa da kasa kayayyakin zamani masu inganci wadanda kuma ke kiyaye muhallin duniya. A halin yanzu, kasar Sin na fitar da motoci amsu amfani da lantarki da baturan Lithium da ma farantan samar da wuta daga hasken rana zuwa kasashe da shiyyoyi sama da 200, wadanda ba ma kawai inganta samar da kayayyaki a duniya suka yi ba, har ma da taimakawa wajen saukaka matsalar hauhawar farashi, tare da bayar da babbar gudummawa wajen tinkarar sauyin yanayin duniya.

A takaice dai, yadda harkokin ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen ketare ya yi ta farfadowa, ya shaida ingancin tattalin arzikin kasar Sin, kuma shi ne dalilin da ya sa wasu hukumomin hada-hadar kudi na duniya, ciki har da Goldman Sachs, suka kyautata hasashensu kan bunkasuwar tattalin arzikinta a shekarar da muke ciki. (Lubabatu Lei)