logo

HAUSA

Wasika daga kwalejin Confucius ta jami’ar koyon ilmi da fasaha ta Durban ta kasar Afirka ta Kudu

2024-09-05 10:13:01 CMG Hausa

Sanele Kervin Ntuli, malami ne a kwalejin Confucius ta jami’ar koyon ilmi da fasaha ta Durban ta kasar Afirka ta Kudu. An kafa kwalejin a shekarar 2013, wato lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar Afirka ta Kudu a karo na farko. Bayan shekaru 10, malamai da dalibai na kwalejin su guda 50 sun aika wata wasika ga Xi Jinping, inda suka bayyana labaransu na koyon Sinanci, gami da nasarorin da suka cimma. Cikin wasikar, sun kuma nuna godiya ga shugaba Xi da gwamnatin kasar Sin, ganin yadda suka samar da damammaki masu kyau ga matasan kasashen Afirka don su cimma burikansu. (Maryam)