logo

HAUSA

Labarin matashi ‘dan kasar Kenya da ya rubutawa Xi Jinping wasika

2024-09-04 19:31:06 CMG Hausa

Wani matashi ‘dan kasar Kenya, wanda ke aiki a hukumar sufurin jirgin kasa tsakanin Mombasa zuwa Nairobi ya zauna a kasar Sin har sau biyu domin kara karatu, da samun horo a fannin injiniyan jiragen kasa, sakamakon aikin inganta layin dogo na Mombasa zuwa Nairobi. La’akari da yadda ya amfana da hakan, matashin da wasu ‘yan ajinsa sun rubutawa shugaban kasar Sin Xi Jinping wasika, inda suka bayyana godiyarsu, daga bisani kuma shugaba Xi ya amsa wasikar ta su, inda ya bayyana cewa, "Ina fatan za ku ci gaba da haskakawa a fannin gudanarwa, da bunkasa layin dogo na Mombasa zuwa Nairobi, da hadin gwiwar kawance tsakanin Sin da Kenya".