logo

HAUSA

Sin da Afirka ’yan uwan juna ne: “Na yarda da likitocin China, abun da ya kawo ni ke nan”

2024-08-27 16:07:38 CMG Hausa

Tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin kashi na 24 dake kunshe da mutane 30, ta tashi a ranar 8 ga watan Yunin shekarar da muke ciki, zuwa Jamhuriyar Nijar, inda suka fara aikin samar da tallafin kiwon lafiya ga mazauna kasar na tsawon shekara daya da rabi. Kwanan nan ne darektan sashin kula da jijiyoyin kwakwalwa na babban asibitin Nijar, ya nemi tawagar ma’aikatan jinya ta kasar Sin, inda a cewarsa, akwai wani maras lafiya dan Nijar, wanda ya bukaci likitocin kasar Sin da su duba lafiyarsa. Sunan mutumin Ma’azou, dan shekaru 48 ne a duniya, wanda aka yi masa tiyata watanni da suka gabata a wani asibitin dake kasar Tunisiya, saboda ciwon kugun da yake fama da shi. Amma bayan wata daya da aka yi masa tiyatar, sai zafin ciwon kugun mai tsanani ya tashi har zuwa jijiyoyi, daga baya zuwa wata na biyar, ciwon kugunsa ya kara tsanani maimakon warkewa, har ma bai iya tafiya da kafafu sosai ba, abun da ya sa Ma’azou da iyalansa suka damu matuka. A karshe, Ma’azou ya zo babban asibitin Nijar don neman taimakon likitocin kasar Sin, inda ya ce: “Na yarda da kwarewar likitocin kasar Sin, abun da ya kawo ni nan ke nan.”

Li Xiaofeng, shi ne mataimakin darekta a sashin kula da ciwon kashi na tawagar likitocin kasar Sin dake Nijar, wanda ya kira wani taron kwararrun likitocin kasar Sin, don nazarin ciwon kugun da malam Ma’azou ya dade yana fama da shi. Kuma bayan da suka duba lafiyarsa da gudanar da bincike cikin tsanaki, da kara fahimtar yadda aka yi masa jinya a baya, likitocin kasar Sin sun tabbatar da cewa, wani nau’in kwayar cuta da ba’a san shi ba ya kama shi bayan da aka yi masa tiyata a kasar Tunisiya. Daga baya, likita Li Xiaofeng, da darektan sashin kula da jijiyoyin kwakwalwa na babban asibitin Nijar, likita Lisr, sun yi shawarwari tare da malam Ma’azou gami da iyalansa, inda suka kudiri aniyar sake yi masa tiyata, da kawar da wurin da kwayar cutar ta shafa, da kuma gudanar da bincike kan nau’in ta. Sai kuma likita Li Xiaofeng ya yi masa tiyata ba tare da wata matsala ba, kuma bayan mako daya, sakamakon binciken ya nuna cewa, malam Ma’azou ya kamu da kwayar cutar Madura, wadda ba safai a kan ga irinta ba, kuma da wuya a yi jinya. Amma likita Li Xiaofeng gami da takwarorin aikinsa na Nijar sun himmatu wajen samar da magani ga malam Ma’azou, kuma kawo yanzu ya samu warkewa sosai, har ma ya iya tafiya da kafafunsa yadda ya kamata. A cewar Ma’azou, su likitocin Sin ne suka ba shi sabuwar rayuwa.

Likita Li Xiaofeng ya ce, yana matukar jin dadin ganin yadda Ma’azou ke samun warkewa, kana yana alfahari sosai da zama daya daga cikin tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin dake ba da taimako a Jamhuriyar Nijar.

Shi ma shugaban tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin dake aiki a Jamhuriyar Nijar, Zheng Zhida ya bayyana cewa:

“Komai matsalolin da muke fuskanta, za mu yi kokarin shawo kansu, don gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata, da bayyana kyawawan halayen likitocin kasar Sin.”

Kasar Sin da kasashen Afirka, aminan hadin-gwiwa ne daga dukkan fannoni kuma bisa manyan tsare-tsare. Tun shekara ta 2015, shirin hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiyar jama’a ya zama daya daga cikin “manyan shirye-shiryen hadin-gwiwa guda 10”, da aka bullo da su a taron kolin Johannesburg na dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC da aka yi a kasar Afirka ta Kudu, har ma a shekara ta 2018, a cikin “muhimman matakai 8” da aka sanar a wajen taron kolin Beijing na dandalin FOCAC, akwai mataki da za’a dauka tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fannin kiwon lafiya. Zuwa shekara ta 2021 kuma, aikin inganta lafiyar dan Adam ya zama na farko a cikin wasu ayyuka guda 9 da aka sanar a taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC. Muna iya cewa, hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannin kiwon lafiya na samun ci gaba babu tsayawa, hadin-gwiwar dake kara samar da alfanu ga al’ummomin kasa da kasa. Kaza lika, a karkashin jagorancin shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannin kiwon lafiya na kara samun damammakin ci gaba.

Idan mun dubi tarihi, za mu gano cewa, kiwon lafiya na daya daga cikin muhimman fannonin hadin-gwiwa da mu’amalar da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Tun shekara ta 1963, kasar Sin ta tura wata tawagar ma’aikatan jinya zuwa kasar Aljeriya, al’amarin da ya bude babin samar da agajin jinya ga kasashen Afirka da kasar Sin ta yi. Kawo yanzu, ma’aikatan jinyar kasar Sin da dama suna nuna himma da kwazo wajen gudanar da ayyukansu a kasashen Afirka daban-daban, wadanda suka taimaka sosai ga karfafa zumunci tsakanin Sin da Afirka.

Sai dai baya ga likitocin kasar Sin dake aiki a kasashen Afirka, a kasar Sin ma, akwai wani likita dan asalin Afirka, wanda ke amfani da fasahohinsa don kulawa da marasa lafiya. Sunan likitan Diarra Boubacar, dan Jamhuriyar Mali ne, wanda ya zama likitan kasar waje na farko da ya samu digiri na uku a fannin nazarin likitancin gargajiya na kasar Sin.

An haifi Diarra Boubacar a shekara ta 1964 a wani gidan likitoci dake Jamhuriyar Mali, wanda ya zo karatu a kasar Sin a shekara ta 1984 bisa tallafin karatu da ya samu, inda ya samu digiri na uku a jami’ar koyon likitanci da magungunan gargajiyar kasar Sin dake birnin Chengdu a shekara ta 1997. Bayan da Diarra ya soma aiki a wani asibitin dake wurin, ya fuskanci matsaloli da dama, wato babu wani maras lafiya da ya je nemansa, saboda shi bako ne dan kasar waje. Yana ta jira yana ta jira, sai wani maras lafiya ya shigo, amma da ganin Diarra, maras lafiya din ya gudu, yana tambaya: “Likitan gargajiya Basine nake nema, me ya sa nake ganin likita dan Afirka a nan?” Diarra ya ce: “Kada ka damu. Ka ba ni dama. Idan ba ka samu sauki ba, ba zan karbi kudinka ba.”

Sannu a hankali, bisa kwarewarsa a fannin samar da jinya, Diarra ya samu amincewa daga mutanen kasar Sin da dama. Kana kuma, yayin da yake karatu da aiki a kasar, shi da tawagarsa sun ziyarci yankunan karkara daban-daban dake lardunan Sichuan da Yunnan, inda ya kara fahimtar matsalolin da marasa lafiya dake wurin suke fuskanta, al’amarin da ya sa ya fara gudanar da ayyukan jin-kai, da samar da jinya ba tare da karbar kudi ba ga masu kamuwa da cutar kanjamau da cutar kuturta, har da samar da horo ga likitoci sama da dubu 3 dake yankunan karkara na tsawon shekaru 10.

Yanzu Diarra ya zama wani likita mai fasahar likitancin gargajiyar kasar Sin da ya yi suna sosai a birnin Chengdu, kuma akwai mutanen kasar da dama dake neman ganinsa don samun magani.

Diarra ya ce: “A rayuwar dan Adam, wata kila zai gamu da matsaloli, wata kila akwai lokacin da ba zai samu amincewa daga saura ba, amma bai kamata ya ji tsoro ba, ya dace ya nuna karfin zuciya da jure wahalhalu. Ina da yakinin cewa, idan wani mutum ya yi kokarin aiki, kwalliya za ta biya kudin sabulu.”

A hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannin kiwon lafiya, akwai mutane da dama masu burgewa, kamar su ma’aikatan jinyar kasar Sin dake samar da taimako a Jamhuriyar Nijar, da likita Diarra Boubacar daga Mali mai fasahar likitancin gargajiyar kasar Sin, wadanda suka bayar da babbar gudummawa ga karfafa zumunta da samun fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Gina muhimman ababen more rayuwa a fannin kiwon lafiya, shi ma wani babban bangare ne da ya samu ci gaba sosai a hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Idan mun tashi cikin mota daga cibiyar Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, muka nufi kudu maso yamma, cikin minti 30 ne za mu isa wani babban gini mai kyan-gani. Wannan ita ce babbar hedikwatar cibiyar shawo kan cututtuka masu yaduwa ta Afirka wato Africa CDC, da kamfanin kasar Sin ya samar da taimakon gina shi. Da ginin nan, da babban ginin hedikwatar kungiyar tarayyar Afirka wato AU, da kasar Sin ta bada taimakon gina shi tun tuni, sun zama muhimman alamu masu jawo hankalin jama’a a birnin Addis Ababa.

Kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna CCECC ne ya dauki nauyin gina babbar hedikwatar Africa CDC, mai fadin murabba’in mita kusan dubu 23.6, wanda ya kammala a watan Janairun shekara ta 2023. Cibiyar nan ta kunshi wasu manyan gine-gine biyu na ofisoshi, da wasu gine-gine biyu na dakunan gwaji, inda ake iya gudanar da ayyuka iri-iri.

A wajen bikin murnar kammala aikin gina babban ginin hedikwatar Africa CDC da aka yi a ranar 11 ga watan Janairun shekara ta 2023, shugaban kwamitin kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat ya yi jawabin cewa, a matsayin nasarar hadin-gwiwar Sin da Afirka, ginin nan ya shaida babban burin bangarorin biyu na kara raya dangantakar abokantaka tsakaninsu, wanda ya bayyana a cikin ayyukanmu na kokarin samar da alfanu don inganta lafiyar al’umma.

Moussa Faki Mahamat ya kara da cewa, hadin-gwiwar Sin da Afirka na da dogon tarihi, wanda ya zama kyakkyawan abun misali. Kuma ginin nan na hedikwatar Africa CDC ya shaida irin wannan hadin-gwiwa a fannin kiwon lafiya. (Murtala Zhang)