’Yan wasan ninkaya na Sin sun nuna karfinsu a gasar Olympics ta Paris
2024-08-07 18:50:09 CMG Hausa
Masu kallonmu, yayin gasar wasannin Olympics dake gudana a birnin Paris na kasar Faransa, kungiyar wasan ninkaya ta kasar Sin ta samu lambobin zinari guda 2, da na azurfa 3 da na tagulla 7, adadin da ya kai matsayin koli cikin tarihi, kuma yawan ’yan wasan da suka lashe lambobin yabo ya kasance mafiya yawa cikin tarihi, kana, abu mai burgewa shi ne, dan wasan ninkaya na kasar Sin Pan Zhanle, ya kafa sabon matsayin bajintar duniya. Amma nasarorin da ‘yan wasan ninkayar kasar Sin suka cimma, musamman ma ganin yadda Pan Zhanle ya kafa sabon matsayin bajintar duniya, sun sa wasu mutanen yammacin duniya su nuna kishinsu, har ma sun fara yada jita-jita. Hakan bai damu ‘yan wasan ninkayar kasar Sin ba, sabo da sun riga sun mai da martani ga wadanda suka nuna shakku kan karfinsu, ta hanyar cimma nasarori a gasar Olympics.