logo

HAUSA

Shugaba Tinubu ya gana da gwamnoni da sarakunan kasar a game da batun zanga-zangar gama gari

2024-07-26 09:46:12 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin jam’iyyarsa ta APC da sarakuna da malaman addinin musulunci da na mujami’un kasar a wani mataki na dakile yunkurin tayar da zaune tsaye da matasan kasar ke yi .

Farko dai shugaban ya fara ganawa ne da gwamnonin sai kuma daga bisani ya gana da sarakuna da shugabannin addinai a lokaci guda, inda ya bukace su da su fadakar da mabiya illolin zanga-zanga tare kuma da kokarin da gwamnati ke yi na daidaita al’amura a kasa baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Taron wanda aka gudanar da shi a fadar shugaban kasa jiya Alhamis 25 ga wata ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima da mashawarcin shugaban kan al’amuran tsaro da sufeto-janaral na ’yan sanda da wasu daga cikin ministocin kasar.

A yayin taron da shugaban ya gudanar da sarakunan da shugabannin addinai, ya kara jaddada irin rawar da za su taka wajen tabbatar da ganin an sami dauwamammen zaman lafiya a kasa baki daya.

Bayan fitowa daga taron ne wasu daga cikin sarakunan suka yi wa manema labarai bayani a game da abubuwan da suka tattauna da shugaban kasa, inda gaba dayansu suka bayyana cewa taron nasu ya fi mayar da hankali game da batun zanga-zanga sai kuma cikakken jawabi da shugaban ya yi musu a kan irin tsare-tsaren da gwamnatinsa take da su da za su inganta rayuwar al’ummar kasa.

Alhaji Ahmed Bamalli shi ne sarkin Zazzau a jihar Kaduna.

“Muna kira ga jama’a da su kara hakuri su yi la’akari da bayanan kwantar da zuciya da ake yi musu, muna da yakinin cewa ba da jimawa ba Najeriya za ta sake komawa kan matsayinta na ja gaba a tsakanin kasashen Afrika.”

Ya tabbatar da cewa, a yayin taron dai dukkannin sarakunan sun shedawa shugaban cewa akwai matukar bukatar a kyautata sha’anin tsaro a kasa baki daya domin kuwa shi ne babbar matsalar da kasar ta fi fuskanta musamman ma arewacin kssar, inda suka shaida masa cewa muddin aka samar da tsaro, mutane za su koma gona, sannan kuma tabbas za a yaki yunwa sannu a hankali. (Garba Abdullahi Bagwai)